Kasuwanci

Kasuwanci

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

00:00
00:00

Episode's summary

Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin jihar Borno da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al'ummar da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita. Bayan kwashe shekaru da dama na rikicin Boko Haram da kuma tasirinsa ga tattalin arziki, gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na neman wata hanya ta bunƙasa tattalin arzikinta da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al'ummarta. Wannan ne ya sa gwamnatin jihar ta haɗu da masu zuba jari da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a wani taro da aka gudanar a Legas, domin duba damar zuba jari da za ta taimaka wajen samar da abin da ake kira durable solutions, wato hanyoyin magance matsalolin al'umma na dogon lokaci. A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta sanar da cimma alkawuran zuba jari har guda tara bayan kammala taron tattaunawa da aka gudanar a Legas Kamfanin Dangote ya ware hannun jari na darajar…

Episodes

411-

Borno na son farfado da tattalin arzikin waɗanda ricikin Boko Haram ya ɗaiɗaita

14 Oct 2026
410-

Rahoton CBN ya ce ƙarfin sayayyar ƴan Najeriya ya ƙaru a watan Satumba

Yau shirin zai mayar da hankali kan sabon rahoton Babban Bankin Nigeria, wanda ya fito da sabbin alkaluman ci gaban da aka samu a fannin damar iya sayen kayayyaki a kasuwanni a tsakanin al’ummar kasar da ya karu da maki 53 a watan Satumba daga maki 52.7 daga watan Agustan da ya gabata. Madallah! Lallai za’a yi cewa, tattalin arzikin Najeriya na farfadowa bisa alƙaluma, amma ga talakan ƙasar, har yanzu babu wani alamun sauƙi. A kasuwanni, farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na ci gaba da kasancewa babban ƙalubale, yayin da ’yan kasuwa ke kokawa da tsadar sufuri da wutar lantarki..

07 Oct 2026
409-

Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya

Sana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya. Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu masu tattara ƙarafa na amfani da ita wajen sayar da kayayyakin da aka sace daga tituna, gadoji, layin dogo da sauran muhimman abubuwan more rayuwa. Wannan ne ya sa wasu gwamnatocin jihohi suka ɗauki matakin dakatarwa ko haramta sana’ar baki ɗaya. Yanzu haka Ƙungiyar masu sana’ar ta jari bola ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi, ta hanyar dakatar da lodi ko sayar wa kamfanoni baraguzai da suke tattarawa. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

30 Sep 2026
408-

Matatar matatar Ɗangote ta ƙaddamar da sayar da hannayen jarinta a hukumance

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko da kansa ya kaɗa ƙararrawar buɗe shigar matatar a hukumance. Matatar ta sanya hannun jari biliyan 4 da miliyan 100 kasuwa, kan Naira 525 ga kowane guda, inda take fatan tara kusan Naira tiriliyan 2 da biliyan 150. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..............

16 Sep 2026
407-

Tasirin da saida hannun jarin matatar man Dangote ke da shi ga al'umma

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........

09 Sep 2026